Tumgik
voahausa · 3 months
Text
Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon ma'aikacin VOA, Kabiru Fagge --BBC Hausa
An wallafa a 13:20 16 Disamba 2023 Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan rasuwar tsohon ma'aikacin gidan radiyon Muryar Amurka, Kabiru Usman Fagge wanda ya rasu ranar Juma'a a Amurka.
Marigayin mai shekara 77 a duniya, ya yi shuhuna tsakanin al'ummar Hausawa a faɗin duniya saboda aikin da ya yi da gidan radiyon Muryar Amurka na kimanin shekara 25.
Cikin wata sanarwar saƙon ta'aziyyar da Tinubu ya fitar, ya jinjina wa marigayin saboda ''taimakawar da ya yi wajen gina ƙasa da kuma taimakon da ya bai wa fannin ilimi'', musamman cikin fitaccen shirin da yake gabatarwa na ''Ilimi Garkuwar Dan'adam' a kowanne mako.
"Muna jinjina masa kan yadda ya zaɓi aikin da yake son yi kuma ya haska ƙimar Najeriya a idon duniya," in ji sanarwar.
Tinubu ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da sauran ɗaukacin al'umar Najeriya da na duniya baki ɗaya.
Source: BBC Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito cewa dan bindigar ya harbe kansa bayan da ya kashe mutanen. via Voice of America Hausa
1 note · View note
voahausa · 2 years
Link
Hukumoin Jamhuriyar Nijar sun bukaci shugabanin matatar man SORAZ su gaggauta yin bitar adadin ma’aikata ‘yan Nijer da ‘yan kasashen waje a ci gaba da shirye shiryen mayarda al’amuran gudanarwar matatar a hannun jami’ai ‘yan Nijer. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Wannan kashedin, ya biyo bayan karancin man da kasar take fuskanta sanadiyyar yaki a kasar Ukraine, inda gangar man fetur ta harba daga dalar Amurka 80 zuwa 123 a yanzu haka. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Yau da Gobe via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Ana zargin Idris da karkatar da sama da naira biliyan 80, lamarin da ya sa hukumar ta EFCC ta tsare shi a tsakiyar watan Mayun da ya gabata. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Kimanin mata Miliyan 2.5 aka yi kiyasin ke mutuwa a Najeriyar sakamokon daukar cikin da ba’a shirya masa ba. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Hukumar ‘yan sandan Ghana ta zargi jakadar Burtaniya a Ghana, Harriet Thompson, da shiga harkar da ba ta shafe ta ba, biyo bayan rubutun da ta yi a kan shafinta na Twita da take bayyana ra’ayinta a kan sake kama mai fafutukar ‘#Fixthe Country’ da aka yi, a hanyarsa ta zuwa kotu. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya dauki matakin raba gardama tsakanin wadanda ke niyar zuwa aikin hajji bana da ministan cikin gida wanda a farko ya kara kudin aikin hajji da sama da miliyan 3 na kudin CFA. via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
Shirin na wannan mako  ya maida hankali ne akan harkokin nakasassun Abuja inda wakiliyar muryar Amurka Medina Dauda ta tantauna da Ibrahim sagir daya daga cikin shugabanin kungiyar masu bukata ta musamman bugo da kari sarkin ‘yan kasuwa nakasassun birnin tarayyar Najeriya. Saurari cikakken shirin sauti:   via Voice of America Hausa
0 notes
voahausa · 2 years
Link
via Voice of America Hausa
0 notes